KannywoodNews

Innalillahi Wainna ilaihirrajiun Wata Mata ta dauko Hayar Yan Daba Suka Caccaka Mijinta Wuka Har Yan Hanjinsa Suka fito, don Zai Kara Aure

Advertising

Innalillahi Wainna ilaihirrajiun Wata Mata ta dauko Hayar Yan Daba Suka Caccaka Mijinta Wuka Har Yan Hanjinsa Suka fito, Saboda Zai Kara Aure a Jihar Kebbi.

Advertising

Jaridar Daily Trust Hausa sun ruwaito rahoton Yadda Wata mata ta dauki hayar yan daba suka kashe Mijinta don kawai Zai kara Aure duk da cewa auren su ya rabu saboda Tsananin kishin ta.

Marigayin me suna Barrister Attahiru Ibrahim Zagga Mazaunin Jahar Kebbi sun rabubda matar tasa ne sakamakon bakin kishi na jahilci data tayar saboda yana shirin kara aure.

Yau saura kwana 7 a daura masa aure da sabuwar amaryansa da zai aura a Maiduguri, to sai shekaran jiya matarsa da suka rabu ta nemo ‘yan ta’adda suka tafi gidansa suka rutsa shi, suka dinga caccaka masa wuka har sai da hanjin cikinsa ya fito.

Advertising

Yan ta’addan sun samu nasaran tserewa, amma ita matar an kamata kafin ta tsere, yanzu haka tana State CID na jihar Kebbi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button