KannywoodNews

Gara Masu Yin Luwadi Da Masu Maulidi – Sheikh Anas Taufik Ghana Ya Kira Ruwa 

Advertising

A wannan satin da yagata malaman Izala da malaman Darika suna maganganu tare da cece-kuce akan wata magana da Sheikh Anas Taufiq Ghana ya fadi cewa, gara kazantar masu Luwadi da kazantar masu Maulidi wanda nan da nan jama’a suka fara masa raddi

Advertising

Hakan ya faru ne a lokacin da malaman Izala suke sassauta ra’ayin kin Maulidi da suke fama da shi a cikin malaman akwai irin su, Nuru Khalid, Dr Ahmad Buk, inda sukayi kira da a sassauta kiyayyar da akewa masu Maulidi.

Domin malaman suna tunanin hakan zai iya kai ga mutum kin Annabi Muhammad (S.A.W), inda a kokarin nuna illar Maulidi da kuma haramta shi da Sheikh Anas Taufiq yake nan da nan furucin nasa ya janyo cece-kuce.

Amma a lokacin da malamin yaji ana ta cece-kucen akan wannan magana da yayi, sai malamin ya bayyana inda yake bayani domin ya fashimtar da al’umma wadanda basu fashimci abin da yake nufi ba.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button