KannywoodMusicNewsUncategorized

Dr Idris Abdulazeez bauchi Ya Karyata Batun Cewa Ya Baiwa Aminu J town Mota da Kyautar Kujerar Makkah

Advertising

Dr Idris Abdulazeez bauchi Ya Karyata Batun Baiwa Aminu J town Mota da Kyautar Kujerar Makkah

Advertising

Fitaccen Malamin Addinin Musuluncin nan Watau Sheikh Idris Abdulazeez bauchi ya fito ya karyata Batun cewa ya baiwa Mawaki Aminu J town Kyautar Hade da Kyautar Kujerar Makkah.

Idan dai masu bibiyar mu a wannan shafi zasu tuna mun ruwaito labarai akan yadda Sheik idris Abdulazeez bauchi ya bayyana cewa Dukkan Yan Kannywood jahilaine babu me Ilimin Addini Acikinsu.

Wannan magana tasa ce tabar baya da kura a Masana’antar ta Kannywood inda wasu daga cikin jaruman sukaita maida martani wa malamin, Sai dai shi mawaki Aminu J town ya kara Jaddada Gaskiyar Maganar da malamin ya fada ne inda shima ya bayyana cewa a Masana’antar Kannywood babu irin zunubin da ba’a aikatawa.

Advertising

Hakan yasa aka bayyana cewa malamin yayi masa kyautar mota hade da Kujerar Makkah wanda hakan kuma ba gaskiya bane

Kalli Cikakken rahoton anan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button