KannywoodMusicNews

Ba ku fi ni son zaman Aure da Sani Danja ba – Mansurah Isah

Advertising

A KARON farko tun bayan mutuwar auren ta da fitaccen jarumi kuma mawaƙi Sani Musa Danja shekara ɗaya da rabi da ta gabata, Mansurah Isah ta fito ta yi hira a kan mutuwar auren. Ta ce komai fa ƙaddara ce daga Allah.

Advertising

A tattaunawar da ta yi da mujallar Fim kwanan nan, tsohuwar jarumar ta bayyana cewa tun bayan rabuwar su da Sani ta ke ganin maganganu kala-kala a game da al’amarin a soshiyal midiya, inda har wasu su na zagi, wasu kuma na nuna ɓacin rai a game da rabuwar da su ka yi.

Mansurah, wadda ke da ‘ya’ya huɗu da Sani – mace ɗaya, maza uku – ta ce ko da farko ma abin da ya sa ta sanar da duniya labarin rabuwar su, ta yi hakan ne domin kada a matsayin ta na fitacciya a gan ta a wani waje ko ta tsaya da wani a riƙa yi mata kallon ta na yin wasa da aure.

Ta ce: “Na san mutane su na sha’awar zaman auren mu, har ma ana kafa misali da mu a cikin ‘yan fim da mu ka shafe tsawon lokaci mu na zaman aure. Don haka rabuwar ba ta yi wa kowa daɗi ba.

Advertising

“To amma mutane su sani, duk rashin jin daɗin su, mu mun fi su rashin jin daɗin hakan saboda mu ne mu ke zaune da juna kuma mu ka rabu.

“Mutane su sani, ba mun yi aure ba ne don mu rabu, domin idan mun yi ne don mu rabu babu yadda za a yi mu shafe shekaru goma sha huɗu mu na tare. Don haka Allah ne ya kawo ƙarshen zaman mu.

“Kuma duk son mu da zama tare, idan aka kawo wajen da zama ya haramta, to dole a yi haƙuri da juna.

“Don haka kamar yadda mutane su ke nuna mana so da ƙauna, kuma su ke yi mana fatan alheri, mu ma mu na yi masu fatan alheri.

“Masu zagi kuma su je su yi ta yi, ba za mu hana su ba.”

Idan masu karatu sun tuna, mujallar Fim ce ta fara ba da labarin mutuwar auren Sani da Mansurah, a ranar 27 ga Mayu, 2021, bayan tsohuwar jarumar ta wallafa sanarwar rabuwar su a Instagram, saƙon da ta goge bayan minti kaɗan.

Tun daga surutai su ka cika kafafen yaɗa labarai kan faruwar al’amarin, kowa na tofa albarkacin bakin sa a kai.

Ita kan ta Mansurah, ta fito ta yi tsokaci a kan maganganun da ake yi, waɗanda har yanzu ba su kau ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button